Me ka ke nema?


Shafin Farko

Abdulrashid Bawa



Abdulrashid Bawa Shugaban EFCC-Najeriay    Hoto: EFCC


Gabatarwa

Shugaban Hukumar Yaƙi da Manyan Laifukan Tattalin Arziƙi da Kuɗaɗe, wato Economic and Financial Crimes Commission (EFCC), Abdulrashid Bawa, mutumin garin Jega ne da ke cikin Jahar Birnin Kebbi a Tarayyar Najeriya.

Abdulrashid Bawa, fasihi, haziƙi, masani, sannan kuma gogaggen mai bankaɗo laifuka ne; wato detective wanda ya samu horo daga fitattun hukumomin binciken laifuka na duniya da suka haɗa da Hukumar Bincike Manyan Laifuka ta Amurka (FBI), Hukumar ‘Yansadan Najeriya, Hukumar ‘Yansanda Farin Kaya ta Najeriya (DSS), Ofishin Yaƙi da Manyan Laifuffuka da Miyagun Ƙwayoyi na Majalisar Ɗinkin Duniya, da sauransu. Tare da haka kuma ya ɗauki shekaru 17 (2004–2021) yana aiki da Hukumar Yaƙi da Manyan Laifukan Tattalin Arziƙi da Kuɗaɗe ta Najeriya (EFCC).

Ƙwarewarsa a wannan fanni na binciken manyan laifuka ta bashi nasarori da dama da suka saka shi samun lambobin yabo da dama wadda mafi girman ciki ita ce ta Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI), biyowa bayan bankaɗo laifukan ƙasa-da-ƙasa da ya yi wadda suka sabauta gurfanar da masu aikata laifuka da dama.

Zamowarsa shugaban wannan hukuma ya maishe shi cirar tutar zamowa shugaban hukuma mafi ƙarancin shekaru a karon farko tun kafa wannan hukuma sannan kuma shugabanta na farko wanda ba ɗansanda ba.

Rumbun Ilimi ya ƙuduri aniyar bin diddigi domin zaƙulo sahihan bayanai game da wannan jarumin matashi, Abdulrashid Bawa, a yi karatu lafiya.

Haihuwa

An haifi Abdulrashid Bawa a ranar 30 ga watan Afirilun shekarar 1980 a garin Jega ta Jahar Kebbi (Ɗado, 2021) a Najeriya.

Karatu

Abdulrashid Bawa ya samu halartar waɗannan makarantu:

  1. Modern Primary School Birnin Kebbi, 1991.
  2. Government Secondary School Owweri, 1997.
  3. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, B.A. Economics, 2001.
  4. EFCC Cadet Officers, course one, 2005.
  5. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Digiri na biyu a Harkokin Ƙasa-daƘasa da kuma Hulɗar Jakadanci (M.S.c, International Affairs and Diplomacy), 2012.
  6. Jami’ar Landan domin neman digiri a fannin lauyanci (Yana cikin yin karatun kenan a halin yanzu bai kai ga kammalawa ba), 2021.


Abdulrashid Bawa Shugaban EFCC-Najeriay    Hoto: Channels TV

Horo

Bawa, ya samu horo (Training) domin ƙwarewa a wannan fanni na Binciken Manyan Laifuka daga Hukumomin da suka yi fice a duniya a wannan fanni. Masu iya Magana suka ce, waƙa daga bakin mai ita ta fi daɗi. Bari mu ji daga bakin Bawa:

“Ni horarren mai binciken manyan laifukan da suka shafi tattalin arziƙi da kuɗaɗe ne wanda kuma nake da zuzzurfar ƙwarewa a fannin bincike, tare kuma da kasancewa ta daga cikin waɗanda suka gurfanar da masu laifuka da dama a gaban kuliya waɗanda suka haɗa da Almundahanar da ta shafi biyan maƙudan kuɗaɗe (Advance fee fraud), rashawar da ta shafi hukuma (official corruption), almundahanar da ta shafi bankuna (bank fraud), satar kuɗaɗen gwamnati da sauran manyan laifukan da suka shafi tattalin arziƙi da kuɗaɗe”.

Bawa, ya cigaba da cewa: “Ni ƙwararre ne a fannin tantance almundahana (Certified Fraud Examiner, CFE), Ƙwararre a Fannin Yaƙi da Satar Kuɗaɗe (Certified Anti-Money Laundering Specialist, CAMS). Ƙari a kan haka kuma, an horas da ni a Hukumar Binciken Laifuka ta Tarayyar Amurka (United States Federal Bureau of Investigation, FBI), Cibiyar Kula da Manyan Laifukan da Suka Shafi Kuɗaɗe ta Tarayyar Amurka (United States Financial Crime Enforcement Network, FINCEN), Bankin Duniya, Ofishi Mai Kula da Manyan Laifuffuka da Abin da ya Shafi Miyagun Ƙwayoyi (The United Nations Office of Drug and Crimes), Rundunar ‘Yansandan Najeriya, Rundunar Jami’an Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (DSS), Makarantar EFCC, da kuma Ƙwararrun Bayar da Horo a Matakin Ƙasa-da-Ƙasa na Birtaniya (United Kingdom’s Global Training Consulting)”, kamar yadda ya zo a Sahara Reporters New York (2020).

Muƙamai

Tun cikin shekarar 2004 Abdulrashid Bawa yake aiki tare da wannan hukuma ta yaƙi da laifukan tattalin arziƙi da kuɗaɗe ta Najeriya. Bisa haka, ya riƙe muƙamai da daman gaske waɗanda suka haɗa da:

  1. Mataimakin Sufirtandan Binciken Laifuka (Assistant Detective Superintendent), 2004.
  2. Muƙaddashin Babban Jami’in Binciken Laifuka (Deputy Chief Detective Superintendent, DCDS), 2016.
  3. Shugaban Sashen, Yaƙi da Cin-Hanci ta Hanyar Kuɗaɗe (Anti-Graft Agency’s Substantive Chairman).
  4. Shugaban Sashen Yaƙi da ‘Yan’ta’adda da Binciken Harkokin Fansho (Head of the Counter-Terrorism and General Investigation/Pension Unit) na Yankin Lagos. Daga Maris 2017 Zuwa Mayu 2018.
  5. Shugaban Yankin Ibadan (Head of Ibadan Zonal Office). Daga Watan Juni 2018 Zuwa Janairu 2019.
  6. Shugaban Ofishin Yankin Fatakwal (Zonal Head, Port Harcourt Zonal Office). Yanki Mai Jahohi Uku; Rivers, Bayelsa da Abia, daga Janairu Zuwa Disambar, 2019.
  7. Shugaban Sashen Haɓɓaka Ƙwarewa na Makarantar EFCC (Head of the Capacity Development Division, EFCC Academy), Abuja, 2019-2020.
  8. Shugaban Ofishin Yankin Lagos, 2020 zuwa 2021. Yankin Hukumar Mafi Yawan Ma’aikata da Suka Kai 604.

Nasarori

Taka waɗancan matakai da kuma riƙe waɗancan gaggan muƙamai, tabbas, dole Bawa ya samu nasarori. Shi da bakinsa ya ce: “Na samu nasarar bincikowa tare kuma da tabbatar da cewa an gurfanar da laifuka masu tarin yawa da suka kai ga matakin yanke hukunci tare kuma da maido da biliyoyin Nairori da miliyoyin Dalolin Amurka a ruwan kuɗi da kuma kadarori a faɗin duniya”, kamar yadda Sahara Reporters New York (2020) suka ruwaito shi yana faɗa.

Thisday Live (2021); Sahara Reporters New York (2020), sun kawo kaɗan daga cikin jerin binciken laifuka da Bawa ya jagoranta cikin nasara:

  1. Bibiyar binciken laifuka sama da 227 da aka gudanar tare kuma da gurfanar da masu laifukan a Yankin Lagos.
  2. Bibiyar dukan bincike da aka gudanar a Yankin Fatakwal da yawansu ya kai 215 tare kuma da samun nasarar karɓo ɗaruruwan kadarorin Gwamnatin Tarayya da suka salwanta.  
  3. Bibiyar binciken dukkan laifukan Yankin Ibadan tare da samun nasarar warware matsaloli 113 da kuma gurfanar da 54 a gaban kuliya a cikin watanni shida.
  4. Aiwatar da binciken badaƙalar tsohuwar ministan man fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke tun daga 2015 zuwa yau (2021). Lamarin da ya samu nasarar ƙwato kadarorin da darajarta ta kai miliyoyin daloli a nan gida Najeriya da kuma wasu ƙasashen da suka haɗa da Birtaniya, Amurka, Daular Larabawa (UAE) wadda a nan Najeriya kaɗai an samu sama da kadarori 92.
  5. Gudanar da binciken badaƙalar kamfani mai suna Atlantic Energy Group  tsawon shekara guda (2014-2015) tare da samun nasarar dawo da dukiyar da kimarta ta kai miliyoyin daloli a nan gida Najeriya da wasu ƙasashen da suka haɗa da Birtaniya, Amurka, Switzerland, Daular Larabawa da kuma Kanada.
  6. Bankaɗo badaƙalar ɗanyen manfetur ta OPA cikin shekara guda (2014-2015) wadda ya kai ga dawo da bilyoyin Nairori.
  7. Binciko Badaƙar Tallafin Manfetur cikin shekaru uku (2012-2015), abin da ya kai shi ga samun nasarar ƙwatowa Najeriya kuɗaɗen da yawansu ya kai Naira biliyan saba’in (70 Billion) tare da gurfanar da kamfanoni masu yawa a gaban kuliya.
  8. Binciken badaƙalar tsohon gwamnan Neja, Dr. Muazu Babangida Aliyu.
  9. A cikin shekarar 2008 ya gudanar da binciken da ya shafi damfara ta kafar Intanet abin da ya kai ga garƙame mutanen da basu gaza sittin (60) ba.

Shugabacin EFCC

Biyowa bayan samun nasarar tantancewa da aka yi masa a Zauren Majalisar Dattawan Najeriya, Bawa, ya zama cikakken shugaban Hukumar Yaƙi da Manyan Laifukan Tattalin Arziƙi da Kuɗaɗe na huɗu a cikin shekarar 2020, sannan kuma mafi ƙarancin shekaru tun farkon kafa hukumar.

Lambobin Yabo

Bawa, ya karɓi lambobin yabo masu tarin yawa a ciki da kuma wajen Najeriya. Kaɗan daga ciki sun haɗa da:

  1. Economic and Financial Crimes Commission Merit Award (2020).
  2. US Federal Bureau of Investigation (U.S. Department of Justice) Recognition Award (2019), for facilitating the collaboration between EFCC and the FBI, which resulted in a mutual fight against Economic and Financial Crimes on an international scale.
  3. US Federal Bureau of Investigation (Criminal Investigative Division) Appreciation (2019) in recognition of his support and contribution in FBI’s Operation rewired, which resulted in nearly 209 arrests worldwide.

Manazarta

Adesomoju A. (2021). PROFILE: Abdulrasheed Bawa to make history as EFCC chairman The 40-year-old who has spent all his work life at EFCC, joined the organisation in 2004. An ciro a 2021, daga https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/443187-profile-abdulrasheed-bawa-to-make-history-as-efcc-chairman.html

Sahara Reporters New York (2021). Meet Abdulrasheed Bawa, the 40-year-old Diezani Inɓestigator Named As EFCC Chairman. An ciro a 2021, daga http://saharareporters.com/2021/02/16/meet-abdulrasheed-bawa-40-year-old-diezani-investigator-named-efcc-chairman

Thisday Liɓe (2021). 10 Things to Know About Abdulrasheed Bawa, EFCC Chair Designate. An ciro a 2021, daga https://www.thisdaylive.com/index.php/2021/02/16/10-things-to-know-about-abdulrasheed-bawa-efcc-chair-designate/

EFCC (2021). A Man on a Mission. An ciro a 2021, daga https://www.efccnigeria.org/efcc/about-efcc-3/executive-chairman

Shafin Tarihi

Najeriya


Shugabannin EFCC:

Majalisun Tarayya:

Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub